Kamfanin dillancin labaran kasar ta saudia WAS ya nakalto wani bayani daga ma’aikatar aikin kasar tana fadar haka a jiya Litinin.
Bayanin ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar ta dakatar bada visar shiga kasar ga masu shigowa kasar daga kasashen Liberia, Salio da kuma Guinea.
A tarayyar Nigeria dai har yanzun maniyyata aikin hajjin bana kimani dubu 76 suna sauraron kasar saudia ta fara bada visar aikin hajji a garesu kamar yadda ta yi alkawari.
Hukumar aikin hajji a tarayyar ta Nigeria ta sanya ranar 6 ga wannan watan na satumba a matsayin ranar da za’a fara jigilar mahajjata zuwa kasar ta Saudia. Sai dai an sami jinkiri wagen bada Visar.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa matsalar na’ura ce a karamin ofishin jakadancin saudia da ke birnin Kano ya hana a fara tanatance passport na mahajjatan, kuma da zarar an warware matsalar za’a fara ba da visar.
Mutum 6 ne kacal suka rasu sanadiyyar cutar Ebola a tarayar Nigeria sannan wasu 15 ne suke jinya, sanadiyyar kamuwa da ita. ABNA